1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministan harkokin wajen Indiya ya yi murabus

October 26, 2012

S. M. Krishna, ministan harkokin wajen Indiya ya yi murabus gabanin gudanar da garambawul

https://p.dw.com/p/16Xrd
Hoto: Reuters

Hakan ya zo ne a daidai lokacin da firaiministan kasar, Manmohan Singh ke shirinn gudanar da garambawul da nufin gyara sunan gwamnatinsa da ke fuskantar dakushewar martabarta sakamakon tabargazar karbar rashawa da ta mamaye ministocin da dama kafin gudanar da zaben majalisar dokokin kasar a shekarar 2014.

Wani jami'i a ofishin firaiministan da ya nemi a sakaya sunansa ya ce a ranar juma'a ne Krishna mai shekari 80 da haifuwa ya mika wa Singh takardar saukarsa daga mukamin ministan harkokin wajen da ya shafe sama da shekaru uku yana rike da shi. Gyare-gyaren da firaiministan ke muradin yi dai na zuwa ne a daidai lokacin da shugbannin jami'yyar Congress da ke mulki ke yin kira ga Rahul Ghandi da ya fito daga tsatson Nehru Ghandi da ya shiga majlisar ministoci.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mohammed Nasiru Awal