1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: Minista Kramp-Karranbaeur ta kama aiki

Gazali Abdou Tasawa
July 24, 2019

Sabuwar Ministar Tsaro ta kasar Jamus Annegret Kramp-Karrenbauer ta sha rantsuwar kama aiki a wannan Laraba a gaban majalisar dokokin kasar.

https://p.dw.com/p/3MfUL
Berlin | Deutsch-Amerikanische Konferenz - Annegret Kramp-Karrenbauer
Hoto: picture-alliance/dpa/W. Kumm

A jawabin da ta gabatar a gaban 'yan majalisar, Minista Kramp-Karrenbauer ta bayyana tanaje-tanajen kasar ta Jamus a game da muraden Kungiyar Tsaron Kasa da Kasa ta NATO kan kudaden da za a ware wa fannin tsaro wanda ta ce zai karu nan zuwa shekara ta 2024 inda ta yi karin bayani tana cewa:

"Dan haka zan aiwatar da burin gwamnatin Jamus na saka kimanin kaso biyu cikin dari na jimilar kudaden da kasar ke samu cikin gida a shekara a fannin tsaro".

A makon da ya gabata ne aka zabi shugabar Jam'iyyar CDU mai mulki a kasar ta Jamus a matsayin sabuwar ministar tsaron kasar domin maye gurbin Ursula von der Leyen wacce aka zaba a matsayin sabuwar shugabar hukumar gudanarwar Kungiyar Tarayyar Turai.