SiyasaJamus
Ministatar wajen Jamus: Babu sulhu da Putin a kan Ukraine
February 24, 2024Talla
Ministatar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta yi watsi da shawarwarin yin sulhun dakatar da yakin Ukraine da shugaban Rasha Vladmir Putin, tana mai cewar a fili take karara Mr Putin ba shi da muradin yarjejeniyar zaman lafiya.
Karin bayani:Jamus za ta ci gaba da taimakon Ukraine
Kamfanin dillancin labaran Jamus DPA ya rawaito Annalena Baerbock na shaidawa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a Juma'ar nan a birnin New York cewa ba za su gajiya ba wajen marawa Ukraine baya, a fafutukar da take wajen kare muradanta na 'yantacciyar kasa.
Karin bayani:Jamus na da nauyin kawo karshen cin zarafi
Ta kara da cewa matukar aka kyale Putin ya ci karensa babu babbaka a Ukraine to babu wanda yake da tabbacin tsira daga mamaya daga Rasha.