1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaZimbabwe

Mnangagwa ya nada dansa a mukamin minista

Mouhamadou Awal Balarabe
September 12, 2023

Dan shugaban kasar Zimbabuwe Emmerson Mnangagwa da dan danginsa daya sun samu manyan mukamai a sabuwar gwamnatin, inda dansa ya zama karamin ministan Kudi yayin da dan danginsa ya zama ministan yawon bude ido.

https://p.dw.com/p/4WG8s
Emmerson Mnangagwa na gudanar da wa'adi na biyu na mulki a ZimbabuweHoto: Tsvangirayi Mukwazh/AP Photo/picture alliance

Fiye da ministoci 30 ne gwamnatin shugaba Mnangagwa ta kusa, inda dansa mai shekaru 34 Kudakwashe David Mnangagwa ya zama karamin ministan Kudi yayin da Dan danginsa Tongai Mnangagwa ya zama ministan yawon bude ido. Sai dai‘yan adawanZimbabuwe sun yi tir da wannan gwamnatin da aka nada wacce ta danganta mafi muni tun bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1980.

Emmerson Mnangagwa na jam'iyyar Zanu-PF da ke mulkin tun bayan samun ‘yancin kai ya gaji Robert Mugabe, wanda aka hambarar a shekara ta 2017, ta hanyar juyin mulki. Amma masu sa ido na kasa da kasa sun bayyana cewar an tafka magudi ababban zabe da ya ba shi damar samun wa'adi na biyu na Mulki.