1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mnangagwa ya zama jagoran jam'iyar Zanu-PF

Abdul-raheem Hassan
December 15, 2017

Jam'iyar Zanu-PF da ke mulki a kasar Zimbabuwe ta tabbatar da sabon shugaban kasar Emmerson Mnangagwa a matsayin jagora kuma dan takara a babban zaben shekarar 2018.

https://p.dw.com/p/2pSdX
Simbabwe neuer Präsident Mnangagwa
Hoto: Getty Images/AFP/T. Karumba

Jam'iyar Zanu-PF ta bayyana wannan mataki ne a yayin babban taron da ta gudanar a karon farko tun bayan takaddamar su da tsohon shugaban kasar, kuma jagoran jam'iyar Robert Mugabe. Matakin jam'yar ya tabbatar da soke kudurinta na baya wanda ya amince da soke Mr. Mugabe a mastayin jagoran jam'iyar.

Sabon jagora jam'iyar kuma shugaban kasar Zimbabuwen Emmerson Mnangagwa, ya ja hankalin sauran shugabannin jam'yar Zanu-PF na ganin ba su maimaita kurakuran da jam'iyar ta tabka a baya ba, kazalika ya kuma sha alwashin ba da hadin kai na ganinan  gudanar da tsabtataccen zabe a shakarar 2018.