Moqtada al-Sadr ya ajiye harkokin siyasa.
February 16, 2014Talla
Shaharren malamin addinin Musulncin nan, mabiyin ɗarikar Shi'a a kasar Iraqi Moqtada al-Sadr, da ya jagoranci yin adawa da kasancewar sojojin Amirka a Iraƙin kafin Amirkan ta janye dakarun nata daga ƙasar, ya bayyana ficewarsa daga dukkan harkokin siyasar kasar.
As-sadr dai ya kasance wani babban mai faɗa a ji a harkokin tafiyar da gwamnatin ƙasar kuma ya ce daga yanzu ya fice daga harkokin siyasa da gwamnatin ƙasar kuma babu wata ƙungiya ko kuma jam'iyya dake wakiltarsu a majalisar dokokin ƙasar da ma ciki da wajen fadar gwamnati, sai dai kuma makarantar da Sadr ɗin ya samar da kuma cibiyar tallafawa mabukata za ta ci gaba da gudana.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Pinaɗo Abdu Waba