Mu'amula tsakanin Musulmi da Kirista a Kenya
December 28, 2016Talla
Wannan kiran Sallah ke'nan a wani Masallacin da ke a wata unguwar da ke a wajen baban birnin Kenya watau Nairobi inda jama'a suka tataru domin yin Sallah, wannan masalaci da ke a Kibera shi ne mafi girma a Kenya,inda matasa suka taru suna yin aiki tare da sauran 'yan uwansu Kirista.Vincent Ayacko kirista ne kuma yana daya daga cikin matasan da suke yin aikin:''Musulmi da Kirista su kan hadu suna yi aikin penti na Masallatai da Coci tare abin gwanin sha'awa.''
Kamar yadda aka yi wa Masallacin penti mai ruwan dorowa haka ita ma Cocin da ke cikin unguwar aka yi mata penti wacce ba ta wucce nisan mita 100 tsakanita da Masallacin ba.