1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mugabe ya cika shekaru 93 da haihuwa

shamsiyya hamza ibrahimFebruary 21, 2017

Shugaban zimbabuwe Robert Mugabe ya shirya gagarumin bikin ranar haihuwarsa. Sai dai wasu 'yan kasar na kokawa game da kashe kudi kan bikin maimakon magance matsalolinsu..

https://p.dw.com/p/2XyLR

Bikin cika shekarun Mugabe 93 a duniya na gudana ne a Matabos da ke da nisan kilomita 600 da Kudu maso yammacin Harare babban birnin Zambabuwe. Kudzai Chipanga wani babban mamba ne a jam´iyar ZANU-PF da ke mulki ya yi karin haske kan  bikin yana mai cewa:  " Shugaba Mugabe mai cetonmu ne kuma mai ceton 'yan Afrika. Don haka muna daraja ranar haihuwarsa, ba zamu so ta wuce mu ba. Mun riki ranar ta zama ranar hutu a kasar". 
 
Sai dai wadansu kungiyoyi da suka yi hadin gwiwa da ake kiransu da "  21 DAYS OF ACTIVISM ZIMBABWE", sun ce tilas ne a soke bikin ranar haihuwar Mugabe a wannan shekarar. Sam Farai Munro guda ne daga cikin mambobin wannan kungiyar, ya ce:"Idan aka duba da gangamin kwanaki 21, ya mayar da hanakali ne kan muhimman abubuwan da ya kamata a ce gwamnati ta yi, ba wai kashe makudan kudi wajen gudanar da shagalin bikin tunawa da ranar haihuwar shugaban kasa ba, bayan kasar na fama da karayar tattalin arziki."

Masassarar tattalin arzikin da Zimbabuwe ta samu kanta a ciki a shekarar da ta gabata  ta sanya gaza biyan ma'aikata albashinsu tun daga watan Nuwamban Shekarar ta 2016 da ya gabata.