Mugabe ya zargi Mujuru da neman kasheshi
December 4, 2014Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe ya yi barazanar gurfanar da mataimakinsa Joice Mujuru a gaban kuliya bisa zarginta da ake yi da yunkurin neman halakashi. A lokacin da yake jawabi a zauren babban taron jam'iyyar Zanu-PF da ke mulki a birnin Harare, Mugabe ya ce ya yi nadamar jerawa da ita Mujuru da ya yi a matsayin mataimakiyar shugabar jam'iyya kana mataimakiyar shugaban kasa a shekara ta 2004.
Tun ma gabanin babban taron na Zanu-PF ne aka dakatar da Joice Mujuru a majalisar koli da jam'iyyar da ke mulki a Zaimbabwe. Sai dai masharhanta na danganta wannan yunkuri da wani yarfe na siyasa don neman mayar da ita sanaiyar weare. Kusoshin jam'iyyar da dama ne ke zawarcin kujerar Mujeru ciki kuwa har da mai dakin Robert Mugabe wato Grace mai shekaru 49 da haihuwa.
Ana jin cewar ministan shari'a Emmerson Mnangaggwa ne za a iya zaba domin ya maye gurbin mukamin mujuru na mataimakin shugaban jam'iyyar Zanu-PF
sa