Muhawara a kan cikakken hankalin Donald Trump
January 6, 2018Talla
Michael Wolff wanda shi ne ya wallafa sabon littafin a kan Donald Trump ya ce shugaban na iya nanata magana daya sau uku a cikin mintoci goma. Sannan ya ce wasu daga cikin na kusa da shugaban na da shakku a game da cewar ko yana da cikakken hankali ta yadda zai iya yin mulki. Sakataran harkokin wajen Amirka Rex Tillerson ya kare shugaban na Amirka daga kallon da ake yi masa na mai tabin hankali yana mai cewar kazafi ne kawai.