1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawara kan Koriya ta arewa da gwajin makaman nukiliya

October 6, 2006
https://p.dw.com/p/BuhB

Kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin duniya na dab da amincewa da daftarin ƙudirin da ƙasar japan ta gabatar na jan kunnen Koriya ta arewa da kuma matakan da zata fuskanta idan ta ta cigaba ta gudanar da gwajin makan ta na nukiliya. Jakadan Japan a Majalisar ɗinkin duniyar Kenzo Oshima, yace zaá miƙa kwafin daftarin ga ƙasashe goma sha biyar dake da wakilci a kwamitin tsaron domin nazari tare da yin yan gyare gyaren da suka kamata. Yace to amma akwai tabbacin kwamitin sulhun zai rattaba amincewa da daftarin a taron da zai gudanar nan gaba kaɗan a yau jumaá. A halin da ake ciki kuma, Rasha ta ce tana tuntuɓar koriya ta arewa domin hana ta gudanar da gwajin makaman nukiliyar da ta shirya yi.