1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawarar 'yan majalisar dokokin Jamus game da sayarwa da Saudiyya makamai

July 6, 2011

Ɗaukacin 'yan adawa a majalisar dokokin Jamus sun fusata tare da baiyana matuƙar mamaki da shirin gwamnati na sayarwa ƙasar Saudiyya tankokin yaƙi guda 200

https://p.dw.com/p/11qYZ
Tankin yaƙi na zamaniHoto: KMW/dpa

Irin wannan kaɗuwa da 'yan majalisar dokokin suka nuna dai, ko kaɗan gwamnatin ba ta tsammaci hakan ba. Dukkan jam'iyyun adawa har ma da jam'iyyun dake cikin ƙawancen gwamnatin sun yi kakkausar suka ga shirin sayarwa da ƙasar ta Saudiyya makamai. Hakazalika Su ma wakilan Chochi da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama da manyan kafofin yaɗa labaru sun soki lamirin shirin cinikin makaman. Sun yi sukar bama kawai ga sayarwa da Saudiyya tankokin yaƙi 200 ba har da abin da suka kira shirun da gwamnatin ta yi.

Gwamnatin dai ba ta fito fili ta bayyana dalilan da suka sanya dacewar sayarwa da Saudiyyan waɗannan makamai ba. A maimakon hakan sai ake nuna cewa gwamnatin za ta taka rawa ta la'akari da muhimman al'amuran dake gudana a yankin. Ɗaya daga cikin dalilan shine daidaita ƙarfi tsakanin Iran da Saudi Arabia, sanin cewa gwamnatin za ta amfana da tasirin ƙasar Saudiyya bayan ta tattauna da Israila. Akan haka ne wani ɗan siyasa na Jam'iyyar SPD Rolf Mützenic ya shaidawa Deutsche Welle cewa " Ina gani wannan hujja ba madogara ba ce. Ina dai tsammanin akwai batu na muradun tattalin arziki da suka shige gaba".

Karte Saudi-Arabien englisch
Taswirar ƙasar SaudiyyaHoto: DW

Ga kamfanin ƙera makamai na Jamus Krauss-Maffei Wegmann da kuma Rheinmetal kuwa wannan ciniki ne mai tsoka. Ƙwararrun masana sun yi ƙiyasin cewa cinikin tankokin yaƙin guda 200 zai tasamma biliyoyin kuɗin euro. 'Yan adawar suka ce cinikin zai yi mummunan illa ga martabar gwamnatin Angela Merkel. Bisa ƙa'idar cinikin makaman dai wajibi ne ƙasar da za'a sayarwa makaman ta kasance mai martaba haƙƙin ɗan Adam ce sannan kuma bata tsunduma kanta cikin wani rikici da ya shafi makamai ba.

Musamman dai masu sukar lamirin cinikin makaman sun yi nuni da rawar da Saudiyya ta taka na tursasawa da cin zarafin masu zanga zanga a makobciyarta ƙasar Bahrain. Renate Kunast shugabar marasa rinjaye ta Jam'iyyar Greens ta yi tambayar shin gwamnati za ta yi watsi ne da haƙƙinta na manufofin ƙetare da kare 'yancin ɗan Adam na ƙasa da ƙasa da goyon bayan dimokraɗiyya domin ribar da kamfanonin ƙera makamai za su samu.

Debatte über Atomausstieg im Bundestag in Berlin
Reanate Kunast ta Jam'iyyar adawa ta GreensHoto: dapd

Shi kuwa Philipp Missfelder kakakin Jam'iyyar Christian Demokrats kan harkokin ƙetare cewa ya yi haƙiƙa wajibi ne a duba muradun Jamus a wannan al'amari. " Idan har gwamnati za ta ɗauki wannan mataki, ina mai ra'ayin cewa zai taimakawa zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wannan zaɓi ne da ya danganci siyasa, kuma haƙiƙa ya ci karo da batun haƙƙin ɗan Adam. To amma duk da haka akwai kuma batu na muradun mu wannan shine abin da ke akwai".

Ga Rolf Mützenich na Jam'iyyar Social Demokrats, hujja ce mai ƙarfi cewa ƙasar Saudi Arabia na cikin yanki da ake fama da rikici. " Ɗauki misali yankin kan iyaka zuwa Yemen akwai tarzomar ƙungiyoyin Salafiyya a ƙasar Saudiyya da rikicin siyasa na cikin gida. Dukka waɗannan na nuni da cewa Saudiyya ba za ta iya zama abokiyar ƙawance ga tsarin da muke gaggawar buƙata ba, ta wanzuwar dimokraɗiyya a ƙasashen labarawa ba.

Gwamnatin Jamus ɗin dai ta yankema kanta cewa ba za ta bada muhimman bayanai ba ga majalisar tsaron ƙasa ta tarayya ba akan cinikin makaman duk da cewa majalisar tsaron ce ta amince da a yi wannan ciniki.

Idan aka duba daga ƙasa ana iya sauraron sautin wannan rahoton.

Mawallafa: Nina Werkhäuser/ Abdullahi Tanko Bala
Edita: Ahmad Tijani Lawal