1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fahimtar kare muhalli na karuwa a Jamus

Yusuf Bala Nayaya
May 28, 2019

Jamusawa daga shekaru 14 zuwa sama na ganin kalubalen muhalli a matsayin gagarumar matsala a cewar ma'aikatar muhalli ta Jamus.

https://p.dw.com/p/3JL2T
Deutschland Umwelt l Demonstration gegen Bayer in Bonn
Wasu masu rajin kare muhalli a birnin BonnHoto: DW/L. Endruweit

Wani rahoton bincike da ya fita a wannan Talata ya nunar da cewa Jamusawa na kara fahimta ta matsalar da ke tattare da sauyin yanayi tun daga shekarar 2016.

Shekaru uku da suka gabata kashi 53 daga cikin dari na Jamusawa daga shekaru 14 zuwa sama na ganin kalubalen muhalli a matsayin gagarumar matsala a cewar ma'aikatar muhalli ta Jamus. Ta kara da cewa adadin a shekarar 2018 kuma ya kai kashi 64 cikin dari.

A cewar Svenja Schulze ministar muhalli a Jamus Jamusawa na ganin ya kamata a gaggauta a ba wa muhalli kariyar da ta dace saboda irin barazanar da yake gani. Ta ce hudu daga cikin Jamusawa biyar sun gane muhimmanci na sauyi daga makamashi da ke gurbata muhalli zuwa wanda baya gurbata muhallin.