Muhimmancin Shafin Facebook a zaɓen Uganda
February 16, 2011'Yan adawa a ƙasar Uganda sun gargaɗi hukumomin ƙasar su tabbatar da adalci a zaɓukan da ƙasar za ta gudanar ranar Jumma'ar dake tafe, ko kuma su fuskanci bore daga matasan ƙasar kwatankwacin na ƙasashen Masar da Tunisia, bisa abinda 'yan adawa suka ce yin anfani da shafukan sada zumunta na Facebook da Twitter da matasan ƙasar ta Uganda ke yi.
Duk da cewar 'yan siyasa a ƙasar Uganda sun himmatu wajen zawarcin ƙuri'un matasa domin zaɓen da zai gudana ranar 18 ga watan Fabrairun nan da muke ciki, galibin matasan ƙasar, waɗanda ke da kaso 60 cikin 100 na yawan al'ummar Uganda na yin ɗari-ɗari game da irin abubuwan da suke sa ran samu daga 'yan siyasar. Akwai dai waɗanda ke ganin rayuwar su za ta inganta, kamar Ruth Nassooba, 'yar shekaru 28 dake gudanar da harkokin kasuwanci a ƙasar:
"Tace ina sa ran samun ci gaba ta fuskar samar da han'yoyi, Ilimi, da kuma baiwa ƙananan yara Ilimin, kana da farfaɗo da asibitocin da suka la'la'ce, da dai sauran ababen more rayuwa. Shi kenan kawa!"
Sai dai kuma akwai waɗanda ke nuna alamar gajiyawa da irin halayen 'yan siyasar, lamarin daya sa basa fatan ganin wani abin yabawa daga gare su. Lulu Jemimmah,'yan shekaru 24 da haihuwa cewa ta yi garin daɗi fa na nesa:
"A gaskiya bana fatan za'a sami wani ci gaba sam-sam, wannan ya danganci yadda kowane mutum ke kallon lamarin ne, haƙika ba na sa ran za'a sami wani sauyi."
A farkon watannan ne majalisar dokokin Uganda ta amince da dokar haramtawa Sarakunan gargajiya shiga cikin harkokin siyasa, abinda kuma 'yan ƙabilar Buganda ba su ji dadin sa ba, kasancewar Basaraken su ya sha nuna adawar sa ga irin matakin. Dan Lubega, wanda matashi ne daga ƙabilar ya ce ba dai jami'iyyar dake mulki ta yi nasara a yankin ba:
"Galibin mutane a Buganda za su ƙauracewa zaɓukan, inda wasu kuma ke cewar za su jefawa masu adawa da shugaba Yoweri Museveni. Muddin ba'a tsaurara matakan tsaro ba, to, kuwa ba za'a sami zaman lafiya a wannan yaki na tsakiyar Uganda ba."
Sai dai kuma ba kowane ɗan ƙabilar Buganda ne ke da wannan ra'ayi ba, domin kuwa a cewar Mr Juuko, wani malamin sakandare a birnin Kampala ba ya hangen wani rikici zai ɓarke:
" Kar ka ambaci wannan yankin da sunan Algeria, ko Code d I'Vore ko kuma Masar. Museveni zai kwantar da duk wani rikici. Babu wanda zai kawo mana matsala anan. Yanayin da ake ciki ba zai sauya ba."
Ko da shike 'yan siyasa a ƙasar Uganda sun rungumi ɗabi'ar yin anfani da shafukan sada zumunta na yanar gizo wajen yaɗa manufofin su ga al'umma domin neman ƙuri'u a zaɓen shugaban ƙasar dake tafe, akwai wasu matasan Uganda da suke bada himma wajen bin shafukan sau da ƙafa, kamar Serene Nyimuri, babbar jami'ar wata ƙungiyar wayar da kan 'yan mata a sha'anin shugabanci da kuma sana'oi a birnin Kampala:
" Ina anfani da shafin Facebook domin zaka iya samun shi, kuma mutum zaifi dogaro da shi akan tashoshin telebijin da radiyo. Kusan kashi 80 cikin 100 na lokacin da nake da shi na yin bincike ne a yanar gizo da kuma yin aikace aikace na a makaranta. Babbar hanyar da nake samun bayanai kenan."
Ba kowane ɗan Uganda ne ke koyi da ɗabi'ar Nyimuri ba, domin kuwa a cikin ƙasar, wadda ke da yawan al'umma miliyan 31,mutane miliyan biyu da rabi ne kawai ke da sukunin samun yanar gizo, kamar bincike ya gano, kana ba kowane mai ziyartar shafukan nema ke nuna damuwa da harkokin 'yan siyasa ba, abinda ya sa wasu ke ganin lokaci bai yi ba tukuna matasan Uganda su yi koyi da Matasan Masar ko na Tunisia.
Mawallafi: Leyla Ndinda/Saleh Umar Saleh
Edita: Usman Shehu Usman