Mummunar gobara: Moria da Tarihinta
Gobara ta kone sansanin 'yan gudun hijira a Moria a kasar Girka. Lamarin ya yi muni matuka. Sai dai tun kafin aukuwar gobarar yanayin sansanin 'yan gudun hijirar mafi girma a Turai ya cika makil.
Tashin gobara a cikin dare
A daren ranar Laraba, wuta ta tashi a wurare da dama a sansanin 'yan gudun hijira na Moria a tsibirin Lesbos na kasar Girka. An dai yi hasashen cewa an ta da gobarar ce da gangan. Wasu mazauna sansanin sun yi magana kan ta’asar. Sai dai akwai wasu rahotanni da ke cewa 'yan gudun hijirar ne suka ta da gobarar da kansu.
Mutane sun bazama tituna
'Yan gudun hijira a sansanin wanda ya cika makil sun yi kokarin tsirar da kansu, a takaice dai ba a sami mutuwa ko jikkata ba. A cewar kafofin yada labaran Girka, mutane da dama sun haye kan bishiyoyi da kuma dazuka a kusa da sansanin. Rahotanni daga masu ba da agaji sun ce dubban jama’a sun yi ta watangaririya a kan tituna babu abinci babu ruwa, yanayin ya yi kamari an shiga rudani.
Kuncin rayuwa
An tsara sansanin zai dauki mutane 2800. A lokacin da wutar ta tashi, akwai mutane 12,600 da ke zaune a sansanin. Yanayin rayuwa a sansanin ya tabarbare tun ma kafin tashin gobarar. Idan aka duba wannan hoton da aka dauka bayan aukuwar gobarar, nan da nan za a fahimci cewa ba za a iya samun rayuwa mai kyau a wurin a nan kusa ba.
Kusa da Turkiyya
Sansanin ‘yan gudun hijirar na Moria yana gabashin tsibirin Lesbos a kasar Girka. Tazararsa da gabar ruwan Turkiyya kilomita 15 ne. Lesbos shi ne tsibiri na uku mafi girma a Girka kuma yana dauke da mutane kusan 90,000. Mutane kimanin 38,000 suke zaune a Mytilini babban birnin tsibirin wanda ba shi da nisa da Moria.
Hoton tauraron dan Adam na wani wurin ajiya
Idan kana son ganin sansanin Moria daga sama ta taswirar “Google Map” to ka yi rashin sa’a. Sansanin gaba daya ba za ka iya gane shi ba. A lokacin da Deutsche Welle ta yi tambaya, bayani na gama gari kawai aka samu “Google ba ya nuna taswirar tauraron dan Adam.“ A maimakon haka, sai dai a yi nuni da hotunan da wani ya samar na tauraron dan Adam.
Hoton da ba a shigar taswirar tauraron dan Adam ba
Wannan horon da aka dauka daga sama – mun zabo wani bangare mai kama da shi – ya nuna sansanin ya bunkasa kwarai da gaske. Yayin da gida mai jan rufi babu kowa a cikinsa kamar yadda hoton tauraron dan Adam na Google ya nuna, bisa ga dukkan alamu sannu a hankali aka maye gurbinsa da wurin ajiyar kayayyaki.
Waiwayen baya
Hotunan titin yankin da aka dauka a watan Disambar 2011. A wancan lokaci babu sansanin ‘yan gudun hijirar, sai dai wata tsohuwar cibiya ta sojoji. A watan Oktoba 2015 ne aka fara rajistar ‘yan gudun hijira a wurin kafin a kai su cikin Girka.
Gajeren lokaci a baya - Dogon lokaci a yanzu
Yayin da a can baya aka tsugunar da ‘yan gudun hijira na gajeren lokaci – wannan hoton da aka dauka a watan Oktobar 2015 – ya nuna an tsawaita wa’adin zaman bisa yarjejeniyar da aka cimma tsakanin EU da Turkiyya a watan Maris na 2016. Tun daga wannan lokaci ake ajiye masu neman mafakar siyasa a nan kafin rarrabasu zuwa sauran kasashen Turai ko kuma a mayar da su kasashensu.
Jira, jira..... jira babu iyaka
Yarjejeniyar EU da Turkiyya na nufin cewa ba za a kai ‘yan gudun hijira cikin Girka ba. Sannan Turkiyya ba za ta mayar da su ba. Tun da kawunan kasashen EU ya rarrabu a kan daukar kason 'yan gudun hijira, a wasu lokutan su kan shafe tsawon lokaci a sansanin. 'Yan kasashe da dama na zaune cikin yanayi maras tsafta a kebabben wuri – ba abin mamaki ba ne da ake samun tashin hankali.
Idan rikici ya tashi
Rikici ya barke tare da tarzoma a watan Satumbar 2016, inda aka sami tashin gobara. A wancan lokaci ‘yan gudun hijira 300 ne kawai a sansanin. Wurare da dama sun kone a sansanin. Wata daya kacal bayan nan wasu daruruwan 'yan gudun hijira suka kona wasu kwantenoni na hukumar kula da 'yan gudun hijira ta EU saboda nuna adawa da tsawon lokaci da ake dauka kafin tantance takardunsu.
Gobara da hasarar rai
An sami aukuwar wata gagarumar gobara a watan Satumbar 2019. A lokacin wasu bishiyoyi ne suka kama da wuta a daura da sansanin ta kuma yadu. Wata gobarar ta sake barkewa a cikin sansani 'yan mintuna 20 bayan nan. Wannan gobarar ta yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu: wata mace da jaririnta. A wannan lokaci 'yan gudun hijira 12,000 ne a sansanin
Soke ziyara
A watan Augustan bana, Armin Laschet Firimiyan jiha mafi girma a Jamus wato North Rhine-Westphalia ya ziyaci Moria. Ya so ya ziyarci wurare da dama a sansanin mai tsananin tsaro. An dage ziyarar cikin gajeren lokaci saboda dalilai na tsaro. Gabanin haka, yanayin ya yi kamari inda suka yi ta rera wakokin 'yanta Moria.
A yanzu kuma?
Sansanin ya cika makil da mutane ga rashin tsafta da matsaloli na lafiya, lamarin ya ta da hankali – sannan a baya bayan nan an sami barkewar corona. Matsanancin hali. Wannan dai kafin tashin gobarar ce. Shin wata babbar matsala ce ke shirin kunno kai ko kuwa wani sabon lamari ne na al’umma da kuma batun muhalli? Kawo yanzu dai babu wani da ke son amsa wannan tambayar?