Murar tsuntsaye a Saudiyya
November 18, 2007Talla
Sakamakon ɓarkewar cutar murar tsuntsaye a kasar Saudi Arabia a ‚yan makonni da suka gabata,hukumomin kasar sun sanar da dokar ta ɓaci a birnin Makka ,tare da kafa komitin dazai kare yaɗuwar wannan cuta.Ma’aikatar kula da harkokin gona da dabbobin kasar,ta aike da sakonni zuwa dukkannin gonakin kiwon kaji kimanin 140 dake wannan gunduwa,dangane da yadda zasu kare gonakinsu daga wannan cuta,data ɓulla a birnin Riyadh.An kuma shwarci masu gonakin kaji da dangoginsu ,da kada su yadda tsuntsayen da suke kiwo,su haɗe da wadanda suka yo kaura.A ranar 15 ga watan Nuwamba nedai,hukumomin saudiyya suka sanarda kashe kaji kimanin dubu a 50 a wata gona ke Al-Kharj,mai tazarar km 150 daga birnin Riyadh.