Murna da juyayi bayan komawa Mosul
Dan jarida mai daukar hoto Khalid Al Mousily ya shiga Mosul tare da Iyalan gidan Ahmad da 'yan IS suka tilastawa yin gudun hijira wanda a yanzu suka koma gida.
Farkawa daga mafarki
An karbe iko da birnin Mosul ya kubuta daga hannun IS a 2017 bayan shafe watannin wanda yakin wanda hakan ya sanya birnin ya yi kaca-kaca. Sannu a hankali mutane na koma birin. Dan jarida mai daukar hoto Khalid Al Mousily ya shiga birnin tare da Mohammed Saleh Ahmad da iyalansa cikin yanayi na farin ciki da juyayi.
Tsakanin kowama da bankwana
Mohammed Saleh Ahmed dan shekaru 31 (a hannun hagu) ya yi shirin komawa Mosul inda ya ke fatan cigaba da rayuwar da a baya ya ke a birnin sai dai kuma dole zai bar sabbin abokan da ya yi a sansanin 'yan gudun hijirar da ya samu mafaka lokacin da ake yaki a Mosul.
Shekara guda a sansanin 'yan gudun hijira
Sansanin 'yan gudun hijira na Al-Hammam al-Alil kenan wanda ya ke a kudu da birnin Mosul. Nan ne Mohammed ya nemi mafaka a loakcin da sojin Amirka suka afkawa yammacin Mosul. Birnin shi ne na karshe da ya kasance a hannun 'yan IS. 'Yan ta'addar sun shiga birnin a shekarar 2014 idan suka tilasta wa mazaunansa ciki kuwa har da Mohammed bin dokokin da suka shimfida.
Yin kaura don fara sabuwar rayuwa
A shekarar da ta gabata Iyalan Mohammed Saleh ba su taba tunanin koma gida Mosul cikin hanzari ba to amma da dama ta samu ba su yi wata-wata ba wajen komawa. 'Yan kwanaki bayan yanke shawarar komawa, makota da 'yan uwa sun tayasu sanya kayansu cikin mota don komowa gida da nufin bude sabon babi a rayuwarsu.
Wakokin bankwana
Iyayen Mohammed ma sun yanke hukuncin komawa gida Mosul. Mahaifin Mohammed wato Saleh Ahmad ya sanya wokoki na Iraki masu sosa rai wanda ke magana kan bankwana da sake hadewa da juna. A hakan ya na kokari ne na nuna irin yadda ya ji lokacin da suka rabu.
Lalata gine-ginen da aka girma tare da su
Bayan da 'yan IS suka fice daga Mosul, yammacin birnin ya kasance a ragargaje. Mohammed (a hannun hagu) ya yi mamakin yadda birnin da ya girma ya zama. A loakcin da ya ke kewayawa wajen baraguzan gine-ginen da suka rushe Mohammed ya ce da ''wuya na ke iya gane komai''.
Komawa rayuwar yau da kullum
Jim kadan bayan komawarsu gida, mai dakin Mohammed wato Iman ta shirya musu abinci dare. Bayan da iyayen Mohammed suka shiga gidan an yi 'yar liyafa ta shan shayi. Duk da cewar gidan ba wani na a zo a gani ba ne amma dai ya fi musu sansanin 'yan gudun hijirar da suka baro. Yanzu suna da kitchen da bandaki. Cikin hanzari mutan gidan sun koma irin rayuwarsu ta yau da kullum.
An maido da kayan wasa
Bayan da Mohammed ya samu aiki a kamfanin gine-gine na kawunsa, ya je ya yi aski da gyaran fuska kana ya dauki yaransa ya kaisu wani sabon wajen wasa da aka bude daga bisani kuma ya tafi ya sayawa matarsa Iman tufafi.
Sabon gida, sabuwar kama
Shi ma mahaifin Mohammed Saled Ahmad ya yi aski da gyaran fuska wanda surukarsa ta taimaka masa wajen yi.