Afghanistan: Musayar wuta a kabul
August 23, 2021A cikin sakon da ta wallafa a shafinta na twitter, rundunar Bundeswehr ta ce jami'in tsaro guda na Afghanistan din ya rasa ransa yayin da wasu uku suka jikkata a harin da ya shafi dakarun Amirka da Jamus. Sai dai babu wani sojan Jamus da ya ji rauni a harin. Rahotanni na nuni da cewa har kawo yanzu, dakarun kasashen waje ba su bayyana karin wa'adin kasancewarsu a kasar daga 31 ga watan Agustan shekarar 2021 ba. A makon da ya gabata ne dai shugaban kasar Amirka Joe Biden ya ce ta yiwu a kara wa'adin domin bai wa dakarun Amirka damar kammala kwashe Amirkawan da ke Afghanistan din baki daya.
Har kawo yanzu akwai sauran dubban Amirkawa a Afghanistan, sai dai kuma kungiyar Taliban da ke da rike a madafun iko a kasar ta ce babu wata sanarwa da ta risketa kan yiwuwar ci gaba da kwashe mutane tare da taimakon dakarun Amirka har zuwa watan Satumba mai kamawa. Tuni dai kasar Ostiraliya ta ce a shirye take ta bayar da tata gudummawar wajen jigilar kwashe mutane a watan Satumbar, idan har Amirka ta kara wa'adin ficewar dakarunta daga Afghanistan din. Kasashen yamma dai na shan suka kan yadda suke tafiyar da aikin kwashe mutanensu daga Afghanistan din, tun bayan da kungiyar Taliban ta amshe ikon kasar.