Musharraf ya kafa dokar ta ɓaci a Pakistan
November 3, 2007Talla
Shugaban Pakistan Pervez Musharraf zai yiwa ´yan kasar jawabi bayan ya kafa dokar ta baci. Wani mashawarcinsa da yaki a ambaci sunansa ya fadawa kamfanin dillancin labarun AFP cewa a jawabin da zai yiwa ´yan kasar a wani lokaci yau din nan shugaba Musharraf zai yi bayani dalla dalla akan dokar da kuma dalilan da suka ya kafa ta. da farko ay au tashsoshin telebijin masu zaman kansu a kasar sun katse watsa shirye shirye bayan jita jitar da aka yada cewa shugaban zai kafa dokar ta baci sakamakon karuwar tashe tashen hankula na ´yan tawayen Taliban da al-Qaida. Yana dai jiran hukuncin kotun kolin kasar a dangane da sahihancin sake zabensa a watan da ya gabata.