1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musharraf zai yi ta zarce a zaɓen ƙasar shugaban Pakistan

September 15, 2007
https://p.dw.com/p/BuBR
Jam´iyar dake jan ragamar mulki a Pakistan ta kammala dukkan shirye shiryen rike shugaban mulkin sojin kasar Janar Pervez Musharraf a matsayin shugaban kasa a wani sabon wa´adi na shekaru 5. Wannan sanarwa da jami´an jam´iyar suka bayar ta zo ne kwana guda kacal bayan da shugabar ´yan adawa Benazir Bhutto ta nuna aniyar ta ta komawa gida don kawo karshen gudun hijirar da ta sa kanta. Bhutto wadda ta bar Pakistan shekaru 8 da suka wuce saboda zargin cin hanci da rashawa ta na tattaunawa da shugaba Musharraf akan yiwuwar hade jam´iyun su don rana madafun iko bayan zabukan da zai gudana a kasar. A jiya juma´a jam´iyar ta ta ba da sanarwa cewa a ranar 18 ga watan oktoba Bhutto zata koma Pakistan domin matsa lamba a maido sahihiyar demokiradiyya. Ba ruwanta da sakamakon tattaunawa batun raba madafun iko da suke da Musharraf mai dasawa da Amirka.