Musulmai sun shirya gangami a Jamus
January 13, 2015A yayin wannan gangami Musulman zasu nuna adawa da shirin kai farmaki da aka kai wa wasu ma'aikatan mujalla a birnin Paris sannan su mika sako ga dubban masu adawa da yawaitar Musulmi a kasar.
Shugaba Joachim Gauck na kasar ta Jamus zai yi jawabi ga taron da misalin karfe biyar na yammaci agogon kasar a birnin Berlin gaban katafariyar kofar nan mai tarihi ta Brandenburg.
Wannan gangami dai cibiyar mabiya addinnin na Islama da ke a nan Jamus ta shirya shi wanda aka yi masa lakabin "Mu zauna da juna dan taimakon kanmu ta'addanci ba da sunanmuba" .
Da yawa cikin mambobin majalisar zartarwar shugaba Markel zasu mara mata baya a wajen wannan gangami dan nuna adawa da masu nuna wa Musulmin kyama daga kungiyar Pegida, inda ta jaddada a jiya Litinin cewa Musulunci wani bangare ne na Jamus.
A jiya dai wadanda suka shiga macin kungiyar ta Pegida sun kai 25,000 a gangamin da suka yi karo na 12 a birnin Dresden.
Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu