Musulmi a duniya na bikin sallah babba
September 12, 2016A yayin da aka gudanar da hawan arfa a ranar Lahadi 11 ga wannan wata na Satumba da muke ciki, a Litinin 12 ga wata ana gudanar da bukukuwan babbar sallah, inda kuma Alhazai zaa su gudanar da jifan shaidan a kasar Saudiyya, aikin da ke zaman cikamakwan ayyyukan da aka wajabta yayin aikin hajji. Al'umma da dama dai na gudanar da jifan shaidan din cike da tsoro da fargaba, kasancewar sa wanda ke cike da hadari saboda cunkoson al'umma yayin gudanar wa.
A aikin hajjin shekarar da ta gabata ta 2015 dai, alhazzai 2,300 ne suka rigamu gidan gaskiya sakamakon wani turmutsitsi da ya wakana a lokacin aikin na jifan shaidan a ranar 24 ga watan Satumba. A kasashen Musulmi da dama inda za a gudanar da bukukuwan sallar layyar za a share tsawon yini ana yanka dabbobi musamman raguna da kuma ziyartar dangi dama aminnan arziki.