Musulmi da Yahudawa sun ziyarci Auschwitz
August 14, 2018Matasa guda 25, Musulmi da Yahudawa da suka hada da 'yan gudun hijira daga kasashen Siriya da Iraki da matasan Yahudawa daga Jamus 'yan shekarun haihuwa tsakanin 17 zuwa 30 suka yi tattaki zuwa gane wa idonsu mummunan babi na tarihin Jamus. Matasan suka ce kwanaki uku da suka yi tare a ziyarar da suka kai a sansanin gwale-gwale na Auschwitz da ke zama wurin ajiye kayakin tarihi na ta'asar da gwamnatin zamanin 'yan Nazi a Jamus ta aikata, ya taimaka wajen kawar da wariya da kyama da ake nunawa juna.
Judith Bartneck daliba ce Bayahudiya a garin Bielefeld da ke nan Jamus da ta yi karin haske, ta ce: "An samu fahimtar juna a tsakanin tawagarmu. Mun yi musayar ra'ayoyi, mun dauki kanmu a matsayin dukkanmu 'yan Adam ne. Addini bai taka wata rawa ta a zo a gani ba. Mun yi magana yadda ake kallon 'yan gudun hijira a Jamus da wasu batutuwa da ba safai ne mutum ke mayar da hankali kansu a rayuwa ta yau da kullum ba."
Yawancin matasan Musulmi da suka yi gudun hijira zuwa Jamus ba su da cikakkiyar masaniya game da addinin Yahudawa saboda haka ne ake samun wasu Musulmin da ke kyamar Yahudawa a Jamus. Masa Alimam 'yar shekaru 17 da haihuwa daga kasar Siriya na a cikin tawagar matasan da suka ziyarci sansanin na Auschwitz, to ko me za ta ce dangane da wannan ziyara da suka yi tare da takwarorinsu Yahudawa?
Ta ce: "A kasar Siriya ba Yahudawa da yawa ko ma in ce ba sa a kasar ne. Wannan shi ne karo na farko da na yi wata haduwa da Yahudawa, kuma gaskiya haduwar ta yi kyau sosai. Wadanda ke cikin tawagarmu mutane kirki ne. Mun yi farin ciki tare mun kuma yi bakin ciki tare."
Babbar majalisar Musulmi a Jamus da Kungiyar Ci-gaban Yahudawa suka shirya wa matasan addinan biyu kai ziyarar a sansanin na Auschwitz da suka ce kwalliya na mayar da kudin sabulu na kokarin kyautata zamantakewa tsakanin Yahudawa da Musulmi a Jamus. Wannan matakin kuwa na samun karbuwa tsakanin 'yan siyasa a Jamus da ke yin kira da aka kara tallafawa, wasu ma kira suke da a mayar da ziyarar zuwa sansanin gwale-gwalen dole tsakanin 'yan gudun hijira.