Corona ta kashe fiye da mutane 60,000 a duniya
April 5, 2020Talla
A cikin jerin kasashe 200 da aka samu bullar cutar a duniya, kasar Amirka ita ce tafi masu dauke da cutar inda yanzu haka kasar ke da mutum 276,000. Kasar Italiya kuwa ita ce cutar tafi kashe mutane inda mutane sama da 14,000 suka salwanta a sakamakon Coronavirus. Jamus na da mutane sama da 90,000 da suka kamu, sai dai cutar ba ta kisa sosai a Jamus kamar yadda take yi a Spain da Italiya da Faransa da Birtaniya.