Yaduwar cuta mai toshe numfashi a China
January 22, 2020Hukumomi a China sun ce an sami karin yaduwar cutar coronavirus mai nasaba da toshewar hanyoyin numfashi inda kawo yanzu mutane 440 suka kamu da ita yayin da yawan wadanda suka rasu a sakamakon kwayar cutar ya kai mutum tara a wannan Laraba.
Mukaddashin daraktan hukumar lafiya ta kasar Li Bin ya shaidawa manema labarai cewa dukkan mace macen sun auku ne a birnin Wuhan da ke gundumar Hubei.
Sabbin alkaluman mace macen na zuwa ne kasa da kwana guda bayan da aka rahoton wani da ya kamu da cutar a Amirka.
Hukumar lafiyar ta sanar da hanyoyin kare yaduwar cutar yayin da miliyoyin jama'a ke zirga zirgar tafiye tafiye a wannan makon saboda hutun sabuwar shekara ta China. Matakan sun hada da feshin magani a filayen jiragen sama da tashoshin jiragen kasa da manyan shagunan kasuwanci.