Mutane 49 sun mutu a fada a Afghanistan
September 17, 2020Kazamin fada tsakanin sojojin Afghanistan da 'yan Taliban ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a gabashin kasar, a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawar sulhu tsakanin bangarorin biyu. Mai magana da yawun gwamnan lardin Nangarhar, Ataullah Khogyani ya ce an kashe dakarun gwamnati 20, yayin da mayakan Taliban 29 suka kwanta dama, 20 kuma suka jikkata. Ya zuwa yanzu dai maharan ba su mayar da martani a hukumance a kan abin da ya faru ba.
Wannan fadan na zuwa ne yayin da gwamnatin Afghanistan da 'yan Taliban suka fara musayyar yawu tsakaninsu a Doha, da nufin kawo karshen rikicin da ya addabi kasar tun daga 2001. Yawancin manyan jami'an Afghanistan sun yi kira da a tsagaita wuta, amma har yanzu kungiyar Taliban ba ta ce uffan a kan wannan bukatar ba.
An samu tsaiko na watanni kafin a fara tattaunawar sulhu a ranar Asabar sakamakon sakarkakiya da aka samu kan musayar fursunoni tsakanin bangarorin biyu.