Mutane a ƙalla 95 suka mutu a ƙasar Brazil sakamakon ambaliya
April 7, 2010Ruwan sama kamar da baƙin kwarya da aka riƙa shekawa a Rio de Janeiro a ƙasar barasiliya wanda suka haɗasa ambaliya da tsakewar ƙasa sun yi sanadiyar mutuwar mutane a ƙalla 95.Masu aiko da rahotanin sun ce a cikin shekaru 30 ba a taɓa samun irin wannan ruwan sama ba a yankin inda a ƙasa da saoii 24 aka samu kusan yawan ruwan saman da ake samu a wata daya waɗanda suka dadatse hanyoyi tare da kawo cikas ga al amuran zirga zirga.Birnin na Rio wanda shine na biyu mafi girma bayan Sao Paulo shine zai karɓi bakoncin gasar cin kofin duniya ta kwalon ƙafa a shekara ta 2014 dakuma wassanin olympics na shekara ta 2016
Yanzu haka dai mutane kamar 1200 suka rasa muhalinsu yayin da wasu dubu goma ke fuskantar barazanar rugujewar gidajensu kamar yadda magajin garin na Rio Eduardo Paes ya ambato, sanan kuma masu bincikke sararin samaniyar sun ce a kwai sauran ruwan saman da kan iya faɗuwa kafin na da wani lokaci a yankin
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Umar Aliyu