Mutane biyu sun mutu a zanga-zangar kenya
June 6, 2016Talla
Mutane biyu sun mutu yayin da wasu shida suka jikata a wata zanga-zanga da ya gudana a birnin Kismu da ke yammacin kasar kenya. 'Yan adawa ne suka shirya wannan sabuwar zanga-zanga don neman gwamnati ta rusa hukumar zaben kasar.
Shaidun gani da ido sun ce jami'an 'yan sanda sun yi harbe-harben kan mai uwa da wabi. Sai dai Sufeto Janar na 'yan sandan kenya Joseph Boinet ya ce sun tarwatsa zanga-zangar saboda haramtacciya ce.
Ya ce "Kotu ta gargadi duk kungiyoyin da ke da niyar shirya-shirya zanga-zanga da su fara neman izini daga hukumomi kasar tukuna. "