Mutane fiye da dubu ɗaya sun mutu a Indiya sakamakon ambaliyar ruwa
August 5, 2007Talla
Ruwan sama mai yawan gaske da ya haddasa ambaliyar ruwa mafi muni cikin shekaru gwammai a yankin kudancin Asiya ya tilasta mutane fiye da miliyan 10 barin muhallansu. Hukumomin dake kula da wannan masifa sun ce ambaliyar ta fi yin muni ne a arewacin kasar Indiya da Bangaldesh da kuma Nepal. A Indiya ka dai jami´an gwamnati sun ce yawan mutanen da suka rasu sakamakon wananna ambaliya yanzu ya kai mutum dubu 1 da 100. Sau da yawa damina a yankin daga watan yuni zuwa satumba ta ka n haddasa ambaliyar ruwa a kudancin Asiya to amma a bana ambaliyar ruwan ta fi yin muni. Hukumomin ba da agaji sun ce ana fama da karancin ruwan sha yayin da mutane da yawa ke fama da cututtuka kamar typhoid da kuma kwalera.