Mutane hudu sun bace a ambaliya a kanada
July 23, 2023‘Yan sanda Kanada sun bayyana cewar mutane hudu da suka hada da kananan yara biyu sun bace, bayan da aka samu ambaliyar ruwa sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a lardin Nova Scotia da ke gabashin kasar. Yaran dai na tafiya ne a cikin wata mota a lokacin da ta nutse, amma wasu mutane uku sun yi nasarar tsira da ransu, kamar yadda rundunar ‘yan sandan kanada ta bayyana. Amma dai ana ci gaba da bincike don gano wadanda suka bace.
Wannan dai shi ne ruwan sama mafi girma da a ka yi a lardin Nova Scotia a cikin fiye da shekaru 50 na baya-bayan nan, inda ambaliyar ruwa ta haddasa barnar da ba ta misaltuwa. Gidajen talabijin sun nuna hotunan hanyoyi da suka rikide zuwa magudanar ruwa yayin da motoci da yawa suka nitse, wasu mutane kuma sauka rasa wutar lantarki a gidajensu. Dama dai wannan lardi ya fuskanci wani iftila'i a karshen watan Mayu, amma na mummunar gobara da ta mamaye dazuzzukan wasu lardunan Kanada da dama.
Gwamnan Nova ScotiaTim Houston ya ayyana dokar ta baci a yankuna da dama na lardin, ya kuma yi kira ga mazauna yankin da kada su shiga aikin neman wadanda suka bace saboda hadarin da ke tattare da wannan mataki.