1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane da dama sun rasa rayukansu a Saudiyya

Lateefa Mustapha Ja'afarSeptember 12, 2015

Sama da 100 ne aka hakikance sun rasa rayukansu yayin wani hadari da ya afku a Masallacin Makka na kasar Saudiyya.

https://p.dw.com/p/1GVMX
Saudi Arabien Mekka Kran Unfall
Hoto: picture-alliance/dpa/AA/O. Bilgin

Jami'an tsaro na farin kaya a Saudiyya wato Civil Defence sun bayyana cewa bayan iska mai karfi da tsawa da ta sa wani injin daga kaya mai nauyi ya fado akan masallaci mai tsarki na Harami a Makka, ya zuwa yanzu hadarin ya hallaka mutane dari da bakwai ya kuma ji wa kusan 240 rauni, a lokacin da suke ibada.

Shugaban na hukumar tsaron ta civil defence Laftanar Suleyman Bin Abdullah Al Amr ya ce za'a gudanar da bincike don gano irin ta'adi da hadarin ya yi da kuma sake duba matakan kiyaye haddura nan gaba a inda ake aikin fadada masallacin, cikin matakan da mahukunta a Saudiyya ke dauka na ganin an rage yawaitar rasa rayuka lokacin ibada saboda cikowa.

Babban masallacin na Harami dai na kewaye ne da ginin Ka'aba wuri mafi tsarki na ibada a addinin musulunci, kuma mafi girma a duniya wanda miliyoyin musulmai ke ziyarta domin gudanar da Aikin Hajji na shekara-shekara.