1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar Robert Mugabe ta mamaye daukacin jaridun Jamus

Lateefa Mustapha Ja'afar AMA
September 13, 2019

A cikin sharhunansu na wannan makon kan nahiyar Afirka jaridun Jamus sun maida hankali kan mutuwar tsohon shugaban Zimbabuwe Robert Mugabe, da nadin mace ta farko a harkokin diflomasiyyar Sudan.

https://p.dw.com/p/3PYcm
Bildergalerie Robert Mugabe Simbabwe Afrika
Marigayi Robert Mugabe na ZimbabuweHoto: picture-alliance/dpa

Za mu fara da jaridar "die tageszeitung"  da ta rubuta sharhinta mai taken: "wata kasa rabu biyu yayin alhini." Da yawa daga cikin al'ummar kasar ba su ji dadin mulkinsa ba, kamar yadda 'yan fansho suka koka. "Ni a wajena ba gwarzo ba ne", in ji wani manomi. A Zimbabuwe babu wanda ba ya sukar marigayi tsohon shugaban kasar Robert Mugabe da ya kwashe shekaru 37 yana mulki.

Wakoki da addu'o'i na tashi a cocin Johane-Masowe da ke Katuma. Maza da mata a wannan gari da ke zaman inda aka haifi stohon shugaban kasar Zimbabuwe Robert Mugabe shekaru 95 din da suka gabata, na yi masa addu'a da fatan da fatan samun rahama bayan mutuwarsa.

Har daf da rasuwarasa a makon da ya gabata, Mugabe ya halarci cocin ta Katolika, bayan raasuwarsa mahalarta cocin sun shiga zaman makoki. Duk da sukan da Mugabe ke sha a wajen al'ummar kasarsa, a wajen tsofaffi, sunai masa kallon mutumin da ya kare rayuwarsa yana mai nemara bakar fata Zimbabue da ma nahiyar Afirka 'yanci, koda kuwa me ya zama daga baya. Mugabe ya rasu a wani asibiti a Singapor, abin da ake alkanatwa da tabarbarewar harkar lafiya a kasarsa sakamakon durkushewar tattalin arziki. 

Fafaroma Francis ya ziyarci kasashen Afirka

Madagaskar Besuch Papst Franziskus
Fafaroma Francis a AntananarivoHoto: AFP/T. Fabi

"Cocin Katolika na kara zama ta 'yan Afirka kuma suna zama masu ra'ayin 'yan mazan jiya," in ji jaridar "Neue Zürcher Zeitung," Jaridar ta ce: A kwanakin baya Fafaroma Francis ya ziyarci kasashen Muzambik da Madagaska da Mauritius. Ya yi batutuwa da suka hadar da na cin hanci da sauyin yanyi da kwararowar hamada da kuma rashin aikin yi. Ya ma tattauna batun sasanta rikicin siyasa da adalci wajen rabon tattalin arzikin kasa a matsayin tushen samuwar zaman lafiya. Rikici tsakanin Muslmi da Kirista na farauwa ne sakamakon matsalar talauci da kuma rashin sanin makama. Abin tambayar shi ne, ma al'ummar Afirka suka yi imani da shi, ganin cewa makomar darikar Katolika da ma addinin Kirista na Afirka. A yanzu kaso 26 cikin 100 na mabiya addinin Kirista 'yan Afirka ne. An yi kiyasin cewa nan da shekara ta 2060, za su karu zuwa kaso 42 cikin 100. 

Mace ta farko a harkokin diflomasiyyar Sudan

Asma Mohamed Abdalla Außenministerin Sudan
Ministar harkokin wajen SudanHoto: AFP/E. Hamid

Bari mu sake komawa ga jaridar "die tageszeitung"  da ta ce "tsohuwar mai neman mafaka ta zama ministar kasashen ketare a Sudan." Jaridar ta ce juyin-yuya halin da aka yi a Sudan ya haifar da samun mace ta farko a wani babban mukami. A karon farko an samu mace a matsayin ministar harkokin kasashen ketare. A karshen mako Asma Mohamed Abdalla da wasu mutane 18 suka yi rantsuwar kama aiki a matsayin ministoci a Sudan. Asmaa ta kasance mace ta uku da ta zamo ministar harkokin kasashen ketare a kasashen Larabawa. Bayan Asmaa Abdallah, akwai ministoci uku mata da suka hadar da ta ilimi mai zurfi da ta bunkasa rayuwar al'umma da kuma ta wasanni. Bayan kifar da agwamnatin stohon shugaban mulkin kama karyaa na Sudan, Omar Hassan Ahmad al-Bashir an kafa gwamnatin rikon kwarya ta hadaka tsakanin sojoji da 'yan adawa, da za ta wakshe watannin 39 tana mulki, kafin daga bisani ta shirya zabe domin mayar da kasar kan turbar dimukuradiyya.