Mwai Kibaki ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a Kenya
December 30, 2007Tun farko kafin sanarda sakamakon zaɓen shugaban adawa Odinga ya fice daga taron manema labaran da aka kira don sanarda sakamakon yana mai zargin Kibaki da sace kuri’u ta hanyar aringizonsu.
Odinga ɗan shekaru 62 da haihuwa kuma ɗaya daga cikin jami’an gwamnatin Kibaki tun farko shi ke kan gaba a kuri’ar jin ra’aoyin jamaa da kuma sakamakon farko na zaɓen da suka fara fitowa,inda a ranar Asabar jam’iyarsa ta baiyana samun nasararsa a zaɓen.
A safiyar Lahadi Odinga ya yi kira ga Kibaki da ya amince da kaye da ya sha yana mai yin kira da a sake kidaya kuri’u.
Sai dai kuma wannan fata ta Odinga bata samu ba tunda hukumar zaɓe ta rigaya ta sanarda nasarar shugaba Kibaki,inda shugaban hukumar zaɓen ya yi kira ga abokan adawa da cewa sakamakon zaɓen ba shine ƙarshen duniya ba,akwai gobe.
Babu kuma wata masaniya ko Odinga zai ƙalubalanci wannan sakamako a gaban kotu,duk da cewa ana sa ran gaggauta rantsar da shugaban kasa da zarar an sanarda sakamakon zabe kamar yadda aka saba a ƙasar ta Kenya.
Masu lura da al’amura dai sunce da wuya a soke sanarwar da hukumar zaɓe tayi. Bayan wannan sanarwar dai magoya bayan Raila Odinga sun kwarara kan tituna suna masu zanga zangar nuna kin amincewarsu da wannan sakamko.
A ranar lahadi kuma an gano gawarwakin wasu mutane 6 a garin Kismu dake yammacin ƙasar,inda magoya bayan Odinga sukayi tarzoma.
Ya zuwa yanzu dai mutane 13 suka rasa rayukansu cikin rikicin zaɓen tun ranar Alhamis.
A yekuwar neman zabensa Kibaki yayi anfani da ci gaba da Kenya ta samu a fannin tattalin arziki shekaru 5 na mulkinsa yayinda a nasa ɓangare Odinga yace jama’a ƙalilan ne suka ci moriyar canjin da Kibaki ya kawo.
Kibaki ya ɗare kujerar shugaban ƙasa na uku ne a 2002 tare da taimakon Odinga,yana kuma da goyon baya na ‘yan kasuwar ƙasar da kuma masu saka jari na ketare.
A shekaru 5 na mulkinsa ya tabbatar da matsayin Kenya na ƙasa da ba yaki,haka kuma ya haɓaka tattalin arzikinta a nahiyar Afrika.
Kibaki ya shiga harkokin siyasa na Kenya ne tun da ta samu yancin kanta daga Birtaniya a 1963.
Yana kuma ɗaya daga cikin membobin komitin da ya tsara kundin tsarin mulkin ƙasar na farko a 1966,ya kuma taɓa rike matsayin ministan ciniki da masaantu na Kenya.
Kibaki da aka haifa a ƙauyen Nyeri dake arewacin Nairobi yana da yara 4 da jikoki da dama.