Muhimancin nada rawani a cikin al'adun Abzinawan a Niger
February 4, 2015Wannan sanannen abu ne musuman cikin kabilun da mafi yawan rayuwar su na cikin karkara , bayan shi kuma nada rawani na da muhimanci a wajen sarakuna da ma manyan Malamai.
Azawa ko nada rawani na da bambanci a tsakanin Kabilu inda ko wace kabila ke da irin nata ,misali a jihar Agadez a wajen Kabilar Abzinawa nadin ko azawa ya sha bambam alal misali nadin ko azawa na abzinawan yankin Air ya sha bambam da na yankin Azawak da dai sauran su.
A duk lokacin da saurayi ba'abzine ya kai shekara 18 , a kan yi baban buki na aza mishi rawani , inda a ke gayyata Manyan Malamai da datijawa , wadanda za su sheda cewa wanan yaron ya shiga sahun manya masu bada shawarwari a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.
Haka zalika diya Matan Abzinawa su ma a lokacin da su kai shekaru 18 a kan yi bukin daura musu Turkudi cewa da dan kwali na Abzinawa , tun daga ranar da a ka daura wa yarinya wanan turkudin ba za a sake ganin kwayar gashin ta ba.