1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Alkinta muhalli da takardu masu daraja

March 2, 2017

Najeriya ta bullo da wani sabon kokari na kare muhalli ta hanyar fitar da takardu masu daraja da zasu baiwa kasar ikon samun kudi har Naira bilyan 20 domin aiwatar da yarjejeniyar birnin Paris da ta sanyawa hannu

https://p.dw.com/p/2YYUm
BG  Greening Morocco's mosques | Solar panels on top of the Koutoubia Mosque in Marrakesh
Hoto: DW/L. Osborne

Wannan sabon tsari da zai taimakawa Najeriyar samun kudadden da take bukata a sawwake domin gudanar da aiyyukan kare muhallinta musamman sauyin yanayi da sannu a hankali ke ci gaba da zama barazana ga alumma, tsari ne da Najeriyar za ta je kasuwar musayar hannayen jari domin sayar da takardu masu daraja da a turance ake kira Bond a kasar.

An dai tsara ma'ikatun muhalli da na samar da hasken wutar lantarki  su kasance cikin wadanda zasu yi amfani da wannan shiri wanda ke cikin alkawarin da Najeriyar ta sanyawa hannu a birnin Paris don kare muhallin, inda za'a fi maida hankali a fanin samar da wutar lantarki ta hanyar da bata lahani da muhalli.

Kenia Kiambu
Muhalli mai ni'imaHoto: DW/A. Wasike

Najeriya ce dai kasar farko a nahiyar Afrika da ta tsara amfani da tsarin takardu masu daraja domin kaiwa ga cimma biyan bukata a wannan fanin. Sanin cewa an tsara shi ne don alkinta muhallin da ya dade yana fuskantar cikas na rashin isassun kudadden gudanarwa, ya sanya mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana muhimmancin wannan.

 "Muna gani wani kawance ne tsakanin sashin samar da kudin gudanarwa da kuma muhalli sassa biyu da a shekaru  da suka gabata ba wanda zai taba tunanen zasu yi aiki tare, bisa wannan tsari na sayar da takardu masu daraja muna sa ran inganta hanyar samar da wutar lantarki da amfani da ita ta hanyar da bata lahanta muhalli, sannan ma'aikatar muhalli na da tsarin dasa itatuwa da zasu kai fadin hecta dubu 131. Wannan ba kawai zai rage samar da hayaki mai lahani ba zai ma samar da  aiyukan yi masu yawa".

Kenia Kiambu
Gida da ke amfani da hasken ranaHoto: DW/A. Wasike

Tuni dai kwararru a fanin muhallin ke hangen alamu na samun nasara daga wannan tsari da shi ne karon farko da Najeriyar ke bullo da shi. Mallam Hussaini Jar Kasa, kwararre ne a fanin muhalli da ke kungiyar Green Thinking  a Abuja.

Ya ce "Wannan tsari yana da kyau kwarai da gaske domin duk abinda za'a kare muhalli to abu ne wanda za'a kare duniya gaba daya, domin muhallin nan yana fuskantar matsaloli da yawa kama daga fari, da yunwa da ma dumamar yanayin kansa, da wannan Najeriya ta kama hanyar shawo kan matsalar".

Abin jira a gani shi ne  aiwatar da shirin da ake wa fatan zai taimaka rage matsalolin muhalli a Najeriyar inda tuni sauyin yanayi da dumamar duniya ke shafar aikin gona da zamantakewar al'umma musamman hasashe na fari da zai jefa rayuwar mutane da dama cikin mawuyacin hali.))