1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dage tattara sakamakon zabe a Najeriya

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 26, 2023

Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Najeriya INEC, ta sanar da dage tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki na tarayya zuwa ranar Litinin.

https://p.dw.com/p/4O0J8
Najeriya | Zabe | 2023 | INEC
Dage tattara sakamakon zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokokin NajeriyaHoto: Patrick Meinhardt/AFP

Ya zuwa lokacin da ta sanar da batun dage tattara sakamakon zaben na jihohi dai, Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta Najeriya INEC ta karbi cikakken sakamkon zabe ne kawai daga jihar Ekiti. Sakamakon farko da hukumar ta INEC ta tattara na nuni da cewa a jihar ta Ekiti, dan takarar jam'iyyar APC mai mulki Bola Tinubu  na da kuri'u dubu 201 da 494 yayin da dan takarar babbar jam'iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar ke biye masa da kuri'u dubu 89 da 554. Shi kuwa Peter Obi na jam'iyyar Labour, ya samu kuri'u dubu 11 da 397. Rahotanni sun nunar da cewa ana sa ran samun sakamakon karshe na zaben da aka gudanar a ranar Asabar din karshen mako, nan da kwanaki biyar masu zuwa.