1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An dakatar da cire tallafin mai

April 28, 2023

Kasa da watanni biyu gabanin zare tallafin man fetur, gwamnatin Najeriya ta ce ta dakatar da shirin da ya dauki lokaci yana jawo cece-kuce a tsakanin al'ummar kasar

https://p.dw.com/p/4QgGJ
Nigeria Tankstelle in Abuja
Hoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

Tuni dai Abujar ta ce ta samo bashi na dalar Amurka miliyan 800 da sunan rage radadin zare tallafin, kuma ta saka farkon watan Yuni domin fara aiwatar da shi a Najeriyar, kasa daya tilo a yankin yammacin Afrika da ke shan man fetur mai araha. Sai dai kuma babu zato babu tsammani Abujar ta ce ta dakatar da zare tallafin har illa ma sha Allahu.

Duk da dumbin asarar da ta kai kusan Triliyan shida ko kuma daya a cikin hudu na daukacin kasafin kudin tarrayar Najeriyar da ke tafiya a sunan tallafi, majalisar tattalin arzikin kasar ta ce batun zare tallafi yana da bukatar ci gaba da zama a cikin kuryar daki .

Najeriya, Layin mai a Abuja
Najeriya, Layin mai a AbujaHoto: AFOLABI SOTUNDE/REUTERS

Maimakon haka dai gwamnatin ta ce za ta sake kafa wani kwamitin da ya kunshi wakilan sabuwa da tsohuwar gwamnatin kasar da zai yi wa batun kallon keke da keke da nufin sanin mataki na gaba, cikin kasar da ke neman fitowa daga rikicin siyasa, amma kuma ke fuskantar barazanar 'yan kodago da ragowar jama'ar gari da ke kartar kasa bisa batun zare tallafin.

Barazanar kuma da a cewar Bala Abdulkadir da ke zaman gwamnan Bauchi kuma daya a cikin yan majalisar ya tilasta wa mahukuntan jinginar da neman zare tallafin.

Koma ya zuwa ina Abujar ke shirin zuwa da nufin kauce wa fushin jama'a, masu mulkin kasar na kallon matsallar tallafin da zama ummul aba'isin kasawar iya kaiwa ga bukatar inganta ababen more rayuwar al'umma.

Kuma ko bayan nan kafa ta wasoso da dukiyar yan kasar a tsakanin jami'an kamfanin mai na kasar da ragowar yan bokon da ke dillancin man fetur.

Najeriya Abuja farashin mai
Najeriya Abuja farashin maiHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Sama da litar man miliyan 60 ne dai Najeriyar ke sha a kullum, adadin kuma da ake dora wa ayar tambaya cikin batun da ke kama da wa kaci ka tashi a al'adar dauri.

To sai dai kuma a fadar Dr Isa Abdullahi da ke zaman kwarrare bisa tattalin arzikin Najeriyar zare tallafin na iya zama zahiri a tarrayar Najeriyar ne in an iya kaiwa ga sauya rayuwar al'ummar kasar.

ita kanta dokar masana'antar man fetur ta kasar dai ta tanadi zare tallafin bayan watanni 18 da fara aiki, a yayin kuma da tuni yan mulkin suka ce ba kasafin tallafin daga farkon watan yuni.

To sai dai kuma  zare tallafin na iya sauya farashin man daga kasa da Naira 200 da Abujar ta ambata a matsayin farashi ya zuwa kusan Naira 700 a kasuwar neman riba. A Najeryar da masu mulkin ke cewar babu damar iya karin albashi.

Kallo dai daga dukkan alamu na shirin koma wa matatun cikin gida da kasar ke fatan kaddamar da aikin nasu na iya kai karshen shigo da tattacen man da kila ma kai wa ga inganta farashi.

.