1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An hallaka 'yan Shi'a 6 a Abuja

Ahmed Salisu
July 22, 2019

Mutane da dama ne aka ba da labarin rasuwarsu sakamakon wata arangama da aka yi da tsakanin 'yan sandan Najeriya da mabiya tafarkin Shi'a a Abuja, fadar gwamnatin kasar. 

https://p.dw.com/p/3MXwP
Nigeria Demo für die Freilassung von Ibraheem Zakzaky
Hoto: picture alliance/AP Photo/Sunday Alamba

Wakilin kamfanin dillancin Faransa na AFP da ke Abuja kana ya shaida faruwar lamarin ya ce ya kidaya gawarwaki shidda baya ga wasu mutane da dama da ya ce sun samu raunuka.

Galibin wanda suka rigamu gidan gaskiya sun rasu biyo bayan harbin bindiga da aka yi musu lokacin da 'yan sandan suka yi kokarin tarwatsa zanga-zangar neman sakin shuagansu da suke kamar yadda wakilin na AFP ya shaida.

A bangaren jami'an tsaron kuma labarin da muke da muke samu na cewar an hallaka wani mataimakin kwamishina 'yan sanda mai suna Umar Usman kamar yadda wakilin DW Hausa a Abuja din Uwais Abubakar Idris ya rawaito mana.

Wannan dai ba shi ne karon farko da 'yan Shi'ar suka yi zanga-zanga makamanciyar wannan ba, don ko a kwanakin bayan sun shiga majalisar dokokin kasar inda nan ma 'yan sanda suka yi artabu da su.