An saki yaran da aka tsare kan zanga zanga
November 5, 2024Yaran suka kwashe fiye da kwanaki 90 suna tsare tun a watan Augusta saboda shiga zanga-zangar tsadar rayuwa da daga tutara kasar Rasha da aka danganta da cin amanar kasa sun shaki iskar ‘yanci ne bayan da babbar kotun da ke Abuja ta sallame su duka.Kotun da ke unguwar Maitama ta cika makil da ‘yan uwa da abokan arziki da ma jami'an gwamnati a zaman da yake shine na karshe da ya samar da ‘yanci ga yaran.
Bayan da lauyan da ke gabatar da kara ya baiyana bukatar gwamnati ta janye tuhumar sai mai sharia Obiora Eguata ya sanar da sallamar yaran bisa cewa sun samu ‘yanci. Suna fitowa suka fara murna da shewa.
Murna dai har baka ga iyayen yaran da suka yi tattaki domin karbar yayan nasu da suka sami 'yanci.
Barrister Abba Hikima shine daya daga cikin lauyoyin da suka kare yaran da aka kamo daga jihar Kano ya shaida cewa bayan sakin yaran akwai sauran magana a kasa.
Kungiyoyin farar hula da masu rajin kare hakokin jama'a da suka je kotun wadanda su ne suka yi ta matsin lamba kafin a kai wannan mataki sun ce akwai sauran gyara.
An dai sanya yaran a motocin safa safa suka kama hanya zuwa jihohinsu da suka hada da Kano da Kaduna. Wannan tuhuma ce da ta dauki hankali sosai tare da haifar da takaddama. Sufeto janar na 'yan sandan Najeriya ya kadammar da bincike a kan abinda ya faru.