Yan sanda sun 'yanto wadanda aka sace
December 15, 2020Yan sanda a Najeriya sun ce sun yi nasarar 'yanto Indiyawan nan biyu da aka yi garkuwa da su a yankin Kudancin kasar a makon jiya. Wani mai magana da yawun rundunar sojin yankin Olugbenga Fadeyi, ya ce an yi musayar wuta a tsakanin 'yan bindiga da jami'an tsaro inda har soja guda ya ji rauni a lokacin da aka yi kokarin 'yanto Indiyawan. Ya ce an gano gawarwakin wasu mutane biyu a cikin dajin bayan da kura ta lafa amma ba tare da yayi karin bayani kan asalinsu ba.
An kama sune a birnin Ibadan a ranar Larabar da ta gabata. Daruruwan Indiyawa na ci gaba da rayuwa a Kudancin Najeriya duk da hadarin fadawa hannun 'yan bindiga da ke kama jama'a musanman 'yan kasashen waje suna neman kudin fansa. A Arewacin Najeriya kuwa, iyaye na cikin zulumi bayan garkuwa da aka yi da 'ya'yansu daga makarantar kwanan nan da ke Kankara a jihar Katsina. Kawo yanzu babu labari a game da halin da suke ciki, face ikirarin Kungiyar Boko Haram na cewa ita tayi garkuwa da daliban su sama da dari uku.