Tafiyar hawainiya a yaki da cin hanci a Najeriya
July 31, 2019A Najeriya kungiyar kare hakin jama'a da yakar cin hanci da rashawa ta Cislac ta kaddamar da wani sabon rahoton da ta yi nazari tare da tattara rahotannin da kafofin yada labaru ke bayarwa a fannin yaki da cin hanci da rashawa, to sai dai duk da wannan ba a ganin muhimmin sauyi a yakar mummunan dabi'ar.
Kungiyar ta Cislac da ta dauki dogon lokaci tana nazari da tattara rahotanin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriyar ta gano muhimmin rawar da kafofin yada labarum suke takawa a wannan fanni ta hanyar yayata masu halin bera da fatan daukan hanyar gyara. Kama daga fannonin ilimi, aikin gona ya zuwa kula da lafiya da ma kwangiloli na muhimman aiki, kusan matsalar ta zama ruwan dare a Najeriyar. Shin me suke fatan cimawa da wannan rahoto ne? Malam Auwal Musa Rafsanjani shi ne shugaban kungiyar ta Cislac ya bayyana cewa.
"Za mu mika wannan rahoto ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa, kuma muna fata majalisun dokokin kasa za su yi amfani da wannan rahoto don tabbatar da ta nemi cikakken bayani daga jami'an gwamnati da kuma yadda ake tafiyar da tsarin gwamnati a Najeriya. Cin hanci da rashawa na kawo babban koma baya ga ci-gaban Najeriya."
Kafofin yada labaru dai sun kasance masu muhimmancin gaske a fannin yaki da masu halin bera a Najeriyar, abin da kungiyar ta ce yayata lamarin ya kai ga bankadowa da ma kwace miliyoyin dukiyar gwamnati da aka yi wa-kaci wa-tashi da ita. To sai dai har yanzu da sauran aiki a gaba bisa ga abubuwan da ke faruwa na mai son kayanka ya fi ka dubara.
Okeke Anya jami'i ne a kungiyar ya bayyana sabbin dubarun da suke bukatar ganin an dauka domin kara yayata yaki da cin hanci musamman ta amfani da harsunan da al'umma ke amfani da su.
"Wannan muhimmin abu ne da zai zamma kyakkyawar hanyar farawa. Shi ya sa idan muka fassara wannan rahoto daga Turanci zuwa harsunan Najeriya, mutane za su ido don ganin shugabanninsu sun yi musu adalci domin yakar cin hanci da rashawa."
Kowacce duba 'yan jaridu ke hasashen za a iya bi domin kara kaimi a aikin yaki da cin hanci a kasar? Malam Musa Adamu dan jarida ne da ke Abuja.
"Dole gwamnati ta san muhimmancin yaki da cin hanci, kuma ta san idan ba ta yi da gaskiya ba mutane suna kallo. Bai kamata gwamnati na yi wa wadanda ba sa tare da ita bita da kulle, amma kuma tana kyale na kusa da ita da su ma ake zargi da cin hanci ba."
A yayin da kungiyar ke zumar yadda za a kara ganin tasirin rahotanin yaki da cin hanci a Najeriya, Cislac na bukatar gwamnati ta hanzarta kafa dokar kare masu kwarmato domin ba da cikakkiyar kariya da za ta iya taimakawa don yakar cin hanci da rashawa.