Najeriya: Cikin bukata, na iya rayuwa babu kudi
Sun tsere daga rikicin Boko Haram, ba su da kudi suna makale a sansanin kula da 'yan gudun hijira. Kowa na bukatar wani abu tsohon kasuwanci ya dawo: ba ni gishiri in ba ka manda. An dauki wannan kasuwanci a hotuna.
Kokarin kashin kai
Ba kullum ne mutane suke samun abin da suke bukata na abinci daga kayan agaji ba. Kudi ko aiki na da wuyar samu a sansanin Bakasi. Sai dai ta hanyar musaya na bani gishiri na baka manda, mutane sun samarwa kansu hanyoyin biyan bukata.
Kudi na nufin cin hanci
"Rashin kudi, Shi ya saka muke haka", inji Umaru Usman Kaski. Yana son yin musayar itacen da ya kai Naira 50 (kimanin centi 11 na Euro) domin ciyar da iyalansa su takwas. Mutane da yawa za su fi son a basu tallafin kudi amma akwai kasada saboda cin hanci ya mamaye matakai da kudaden za su bi.
Musanyen tsabar shinkafa da masara
Fiye da shekaru takwas 'yan Boko Haram suna ta'addanci a yankin arewa maso gabashin Najeriya. Kimanin mutane milyan biyu suka tsere wasu sassan Najeriya ko kasashen ketere. Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin ya haifar da daya daga cikin aikin jinkai mafi girma a duniya. Anan 'yan gudun hijira: Falmata Madu ta na musayar tsabar shinkafa domin samun masara daga Hadiza Adamu.
Girma kamar karamin gari
Akwai 'yan gudun hijira 670,000 a sansanonin da suke yankin arewa maso gabashin Najeriya. A sansanin Bakasi da ke wajen birnin Maiduguri akwai kimanin mutane 21,000. Ga Falmata Adamu ta bayar da Masara domin samun ganyen alaiyaho daga wajen Musa Ali Wala.
Babu wani abu na daban
A zahiri Abdulwahab Abdullah ba kasafai yake son kifi ba. Amma kananan kifi ne kadai zai iya saye saboda tsadar kayayyaki. Busashen kifin ya kai Naira 150 (kwatankwacin centi 36 na kudin Euro), Mutumin mai shekaru 50 da haihuya ya shafe shekaru uku a sansanin, yana bukatar samun mai.
Bukatar chanji
Nariru Buba (wanda yake hannun dama a hoto) yana da "omo" na wanki wanda ya sayo bayan ya yi aiki a gari. A Lokacin ba ya bukatar wani abu na musamman. Wannan akwai banbanci saboda yana bukatar gyada cikin gaggawa, amma ba shi da kudi. Matata ta haihu babu babu nono" inji Buba. Gyada zatai taimaka mata samun ruwan nono.
Ba karshen abin da ake gani
Maiduguri fadar gwamnatin Jihar Borno na zama tungar Boko Haram cibiyar tashe-tashen hankula. Lokacin hutun Kirsimeti 'yan ta'adda sun kashe kimanin mutane tara sakamakon hari. Babu alama 'yan gudun hijira na sansanin Bakasi za su koma gida. Ga alama za a ci gaba da wannan musaya kamar ake gani a wannan hoto mata na musayar Taliya da waken soya.