Mutum na farko ya mutu a sakamakon coronavirus
March 23, 2020Hukumomin kasar dai sun ce mutumen mai shekaru 67 a duniya ya mutu da cutar ne bayan an shigo da shi a kasar daga Birtaniya inda ya jima yana fama da cutar sikari, kan daga bisani rshin lafiyarsa ta kara tsananta.
Wannan dai shi ne mutun na farko da ya mutu a Najeriya da cutar ta Covid-19 tun bayan bullarta a kasar, inda a yau Litinin hukumar ta NCDC mai lura da cututuka ta bayyana mtun akalla 36 da kamuwa da ita galibi a jihar Legas mai cinkoson mutane fiye da mililan 20.
Daukacin kasashen nahiyar Afirka dai ya zuwa alkaluman da kamfanin dillancin labaran Faransa AFp ke tattarawa sun nuni da cewar mutun dubu daya da 300 suka kamu inda wasu kimanin 40 suka rigamu gidan gaskiya duk da matakan kariya da wasu kasashen ke ci gaba da dauka a ko ina.