1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Coronavirus ta janyo tsaiko a aikin layin dogo

Binta Aliyu Zurmi
March 6, 2020

Ministan Sufuri a tarayar Najeriya Rotimi Amaechi, ya ce  za a sami tsaiko a ayyukan layin dogo da aka fara daga jihar Legas zuwa jihar Ibadan mai nisan kilomita 150, a sabili da barkewar cutar nan ta Coronavirus.

https://p.dw.com/p/3Yzf8
Nigeria Eröffnung Eisenbahnlinie zwischen Abuja und Kaduna
Hoto: DW/U. Musa

Ministan ya kara da cewar ma'aikatan da suka tafi gida hutun sabuwar shekararsu, sun makale ne bayan da Coronavirus tai kamari,  aiki da ya kamata a kamala shi a watan Mayun da ke tafe bisa dukkan alamu hakan ba zai yiwu ba.

Ya zuwa yanzu dai wannan annobar Coronavirus ta janyo asara mai yawa a fani daban-daban na alamuran yau da kullum. Yanzu mutum dubu dari ne suka kamu da cutar a fadin duniya, yayin da sama da mutum dubu uku suka mutu a sanadiyarta. 

Kasashe hudu dake a Kudu da sahara suka sami bullar cutar sai dai ba tai kamari ba duk kuwa da mu'amalar da ke tsakanin China da kasashen.