Najeriya: Fara ba da sabbin kudi ta kan kanta
February 2, 2023Matakin babban bankin Najeriya CBN na zuwa ne a daidai lokacin da harkokin kasuwanci suka fara galabaita a wasu yankunan kasar, lamarin da ya janyo bacin ran miliyoyin jama'a a yayin da ya rage kasa da makonni hudu a je ga babban zaben kasar. To sai dai shugaban bankin Mista Godwin Emefiele ya ba da umarnin da a ba wa ko wani kwastoma da ke da bukatar kudi, naira dubu 20 kadai a ko wace rana.
Kafin zuwan wannan matakin dai an sha fama da cunkoson jama'a a guraren injinan cirar kudi na ATM a duk sassan Najeriya musanman a biranen Legas da Abuja fadar gwamnatin kasar, inda jama'a ke share dogon lokaci suna jira, kafin su kai ga cirar sabin takardun kudin.
A watan Oktoban bara ne dai babban bankin Najeriya ya sanar da canja wasu daga cikin takardun kudin kasar tare da bayar da gajeren wa'adi na janye tsaffin takardun kudin.