1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Gomman mutane sun kamu da kyandar biri

May 30, 2022

Hukumar dakile cutttuka masu yaduwa ta Najeriya ta tabbatar da cewa mutane 21 ne suka kamu da cutar Kyandar biri a kasar.

https://p.dw.com/p/4C1Zn
Birrai
Hoto: Nasir Kachroo/NurPhoto/imago images

Rahoton hukumar ya kuma bayyana cewa tuni mutum daya ya mutu sanadiyar cutar. Tara daga cikin wadanda suka kamu da cutar mazauna birnin Abuja ne, da ke zama babban birnin kasar.

Hukumar ta ce tun a watan Janairun da ya gabata suka zargi cewa mutane 61 sun kamu da cutar. A Nahiyar Afirka, an fi samun bullar cutar ta kyandar biri a kasashen Kamaru da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango da ma Najeriyar. A baya.-bayan nan cutar ta haifar da fargaba, inda aka tabbatar da fiye da mutane 200 sun kamu da ita a kasashe 19, wanda yawanci kasashen Turai ne.