1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta sa gwamna ya koma Auno

May 11, 2020

Yayin da mayakan Boko Haram suka zafafa hare-haren da su ke kai wa a kauyukan da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, gwamman jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya mayar da ofoshinsa zuwa garin Auno.

https://p.dw.com/p/3c1tO
Afrika Nigeria Borno Professor Babagana Umara Zulum
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara ZulumHoto: Government House, Maiduguri, Borno State

Kusan kullum ana samun rahotanni na kai hare-hare a kauyukan da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, wadanda kuma ba su da nisa daga Maidugurin da ke zama fadar gwamnatin jihar Borno a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya. Wadannan hare-hare dai na kara mayar da hannun agogo baya a kokarin tabbatar tsaro da zaman lafiya a wannan yankin, abin da ya sa mutanen kauyukan tserewa zuwa Maiduguri, inda ake kara fuskantar kalubalen ayyukan jin kai ga kuma barazanar da cutar COVID-19 ke yi.

Gwamna ya koma Auno

Bisa wannan dalilin ne gwamnan jihar Bornon Farfesa Babagana Umara Zulum ya bude wani ofshinsa na wucin gadi a garin Auno da ke da nisan kilomita 20 daga Maiduguri fadar gwamnatin jihar, kana guda daga cikin garuruwan da a 'yan kwanakin nan suka fi shan azabar hare-haren mayakan Boko Haram.

Mutmaßlicher Boko-Haram-Angriff in Nigeria
Hare-haren sari ka nokeHoto: picture-alliance/AP/Jossy Ola

Masana da masharhanta da ma al'ummar jihar, na bayyana farin ciki kan wannan mataki na gwamnan da suke ganin zai yi tasiri wajen tabbatar da tsaro a yankin da ke fama da matsalar tsaro. Malam Isma'il Mustapha mai fashin baki ne kan harkokin tsaro, a cewarsa zaman da gwamnan zai yi a wannan yankin zai sanya dole a samar da tsaron da ya kamata. Ita ma Malama Baraka Umar cewa ta yi matakin gwamman ya nuna cewa yana kishin al'ummarsa, kuma hakan zai tabbatar da tsaro a yankin.

Matakin da ya dace

Ali baba Adamu kuwa cewa ya yi zaman gwamman a wannan wuri zai bai wa su kansu mutanen kauyukan kwarin guiwa, na zama a garuruwansu maimakon tserewa da su ke yi. A nasu bangaren, kungiyoyin fararen hula na shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriyar na cewa haka ya kamata, kuma dama burinsu shugabanni su kasance kusa da al'ummarsu. Masu fashin baki dai, sun nemi a bai wa gwamman hadin kai ta yadda zai samu nasarar wannan mataki da ya dauka, kuma sun yi fatan jami'an tsaro ma za su bayar da tasu gudummawar, wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin.