1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Gwamnati ta haramta kungiyar Biafra

September 20, 2017

Kama daga shugaban majalisar dattawa na kasar da sauran duk masu fada a ji na kallon haramci kan kungiyar ta IPOB mai rajin kafa kasar Biafra da cewar bai cika sharuda ba sannan kuma ba ya bisa hanya.

https://p.dw.com/p/2kOmY
Nnamdi Kanu Jagoran kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra
Nnamdi Kanu Jagoran kungiyar masu rajin kafa kasar BiafraHoto: DW/K. Gänsler

Ministan labarai na Najeriya Alhaji Lai Mohammed dai ya ce tuni shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan shirin dokar haramta kungiyar abin kuma da ke da matukar muhimmanci ga kokari na kwantar da hankula cikin kasar,lamarin ya fara tsokacin da martanin jama'ar kasar. To sai dai kuma ko bayan  rattaba hannu na shugaban kasar a kan dokar ma'aikatar, shari'a ta kasar ta samo wani umarnin kotun da ya tabbatar da haramcin kungiyar. Abubakar Malami ministan shari'a na kasar ya ce wannan mataki da gwamnatin ta dauka na zaman  babbar nasara a kan hanyar kai karshe na kungiyar.

A cikin kwanakin da suka gabata magoya bayan kungiyar ta IPOB sun yi ta kai hare-hare a kan sojoji da kuma tsirarun Hausawan da ke zaune a yankin kudu maso gabashi na Najeriyar.