1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Harin kunar bakin wake ya janyo asarar rayuka

August 16, 2017

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 16 da kuma wasu 82 da suka jikkata a wasu jerin hare-haren kunar bakin wake da aka kai a kauyen Mandurari na jihar Borno.

https://p.dw.com/p/2iKYy
Nigeria Konduga Selbstmord-Attentat
Hoto: Getty Images/AFP

Hare-haren kunar bakin wake da aka kai a wata kasuwar dabbobi da ke a kauyen Mandurari na karamar hukumar Konduga a jihar Borno sun yi sanadiyyar mutuwar mutane 16 sannan 82 suka samu raunuka a cewar rundunar 'yan sandan Najeriya. A wani gajeren sako da ya aike wa manema labarai dangane da hare-haren kwamishinan 'yan sanda a jihar Mista Damian Chukwu ya ce mata biyu da wani matashi guda ne suka kai wadannan hare-hare da maraicen ranar Talata. Ya ce tuni aka kwaso wadanda suka samu rauni dabam-dabam zuwa asibiti a garin Maiduguri don samun kulawar likita. Rundunar kuma ta tura jami'anta na sashen kula da tashin bama-bamai zuwa wurin da abin da ya faru don tabbatar an kare lafiyar sauran al'ummar wurin. Kwamishinan 'yan sanda ya kuma ce kura ta lafa a yankin ya zuwa wannan lokaci.

Selbstmordanschlag in Maiduguri, Nigeria
Harin kunar bakin wake ya zama ruwan dare a jihar Borno, kamar wannan da ya auku a wata kasuwar shanu a Maiduguri a shekarar 2015Hoto: AFP/Getty Images/Stringer

A daya bangaren kuwa wata majiya daga asibiti da kuma al'ummar garin sun bayyana cewa mutanen da suka mutu sun kai 28 inda ake fargabar alkaluman za su iya karuwa duba da yanayin da wasu da ke kwance a asibitin ke ciki.

Yawaita kai hare-hare a Arewa maso Gabas

Wannan hari dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan da mayakan Boko Haram suka hallaka wasu mutane hudu tare da kona kauyen Amarwa da ke kusa da kauyen Mandurari mai nisan kilomita 25 daga Maiduguri fadar gwamnatin jihar.

Kungiyoyin agaji da sauran al'ummar yankin na bayyana damuwa na karuwar irin wadannan hare-hare musamman wanda ake nufin 'yan gudun hijira, inda suka bukaci gwamnati da jami'an tsaro da su rubanya kokarinsu wajen ganin an magance wannan matsala ta tsaro.

Gwamnatin tarayyar Najeriya dai ta umurci manyan hafsoshin tsaron kasar da su koma Maidugiri da zama domin fuskantar yaki da kungiyar Boko Haram.