1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar tallafin man fetur a Najeriya

January 20, 2022

Majalisar tattalin arzikin Najeriya ta kamalla wani taro a Abuja ba tare da yanke hukunci a kan zare tallafin man fetur da ke jawo kace-nace cikin kasar a halin yanzu.

https://p.dw.com/p/45rAg
Matatar man fetur a Najeriya
Karancin matatun man fetur, na zaman guda daga kalubalen NajeriyaHoto: Construction Photography/Photoshot/picture alliance

Batun na tallafin man fetur dai na da kalar baki a idanun 'yan mulkin Tarayyar Najeriyar da ke kallon kudin batarwa daga harkar man fetur, amma kuma tallafin da kasar ke biya yake cinye su. Duk da cewar dai sun dau kusan tsawon shekara guda suna nazarin mafita, har ma majiyoyi sun ce sun kai ga amincewa da sabon farashin Naira 302 kan kowace litar man dai, taron majalisar tattalin arzikin kasar a Abuja ya kammala ba tare da iya bayyana hukuncin majalisar kan makomar tallafin man fetur din ba.

Karin Bayani: Najeriya ta ci ribar man fetur a karon farko cikin shekaru 44

Majalisar ga dukkan alamu na shirin fakewa da dokar masana'antar man fetur da ta bai wa kamfanin NNPC iko na gashin kai, ta shaidawa manema labarai cewar har yanzu ba ta kammala nazari kan batun na tallafi da kasar ke fadin asara ce babba ba. Godwin Nogheghase Obaseki dai na zaman gwamnan jihar Edo, daya kuma a cikin mahalarta taron da ya ce majalisar tattalin arzikin ta dauki fiye da shekara guda tana nazari kan batun tallafin na man fetur.

Najeriya Abuja Farashin man fetur
Duk da kasancewar Najeriya guda daga cikin mabobin OPEC, ana samun karancin feturHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

A cewarsa akwai kwamitin da majalisar ta nada a karkashin gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad el-Rufai kuma ya yi aiki a kan rahoton makomar tallafin da ya tabbatar dad cewar Najeriyar na sayar da man a kan Naira 162 a yayin da kusan daukacin makwabtanta ke ninka farashi, kuma ana tafka asara sosai wajen bayar da tallafin. Ya kara da cewa za a iya amfani da makudan kudin da ake yin asararsu wajen gina hanyoyi da samun ilimi. Ga wannan majalisar dai muhawarar ita ce ko su ci gaba da kisan kudin da babu su domin tallafawa masu motocin hawa ko kuma su dakatar.

Karin Bayani: Matatun mai masu zaman kansu a Najeriya

Obaseki ya ce lokacin da suka yi nazarin batun tallafin, sun ga daya a cikin uku na jihohin kasar ne ke shanye biyu bisa uku na tattalafin da ake batu, kuma ana bukatar adalci. Duk wadannan batutuwa an kawo wa majalisa kuma tasha tattaunawa, yanzu tana kan tattaunawa babu hukunci kan batun tallafin na man fetur. Sai dai kuma an bai wa shugaban kasa rahoton kwamitin, abun da ya faru ke nan a cewar Obaseki.